Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Majalisar Dokokin Somalia Sun Tsige Firai Minista Hassan Khayre


Firai Ministan Somalia Hassan Ali Khayre

‘Yan Majalisar Dokokin Somalia sun tsige Firai Ministan kasar Hassan Ali Khayre a wata kuri’a ta rashin tabbas ta ba zata da suka kada akansa, a cewar shugaban Majalisar Dokokin kasar.

A lokacin wani taron manema labarai a ranar Asabar 25 ga watan Yuli bayan kada kuri’ar, Mohamed Mursal Abdulrahaman, ya zargi gwamnatin Firai Minista Hassan Ali Khaayre da kasa tabuka “abun a zo a gani.”

“Yan majalisa 170 ne suka kada kuri’ar goyon bayan kudurin tsige Firai Ministan, wasu guda 8 kuma suka yi akasin haka,” a cewar shugaban Majalisar. “A saboda haka, an zartar da kudurin, kuma muna yin kira ga Shugaban Somalia da ya nada sabon Firai Minista.”

Shugaban Majalisar ya zargi Firai Minista Khayre da gwamnatinsa da kasa cika alkawuran da suka yi wa ‘yan kasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG