Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Majalisar Sarki 5 Sun Yi Murabus a Zamfara


Masarautar Shinkafi dake Jihar Zamfara a arewacin Najeriya, ta nada Femi Fani kayode, tsohon Ministan Sufurin Jirgin Saman Najeriya a matsayin sarautar Sadaukin Shinkafi, lamarin da bai yiwa al’ummar Shinkafi dadi ba.

‘Yan majalisar Sarkin su biyar sun yi murabus don nuna adawa da nadin da Sarki Muhammad Makwashe yayi.

Dr. Tijjani Salihu daya daga cikin ‘yan majalisar sarki, kuma malami a jami’ar Usman Dan Fodio Sokoto, ya shaidawa wakilin muryar Amurka cewa, yayi murabus daga mukaminsa na "Uban Marayun Shinkafi" saboda a cewar sa an baiwa makiyin arewacin Najeriya sarauta, kuma mai yawan sukar sarkin Musulmi, kuma hakan abin bakin ciki ne.

Shi ma Alhaji Sulaiman Shu’aibu, wanda yayi murabus daga mukamin sa na "sarkin Shannun Shinkafi", ya bayyana wa wakilin muryar Amurka dalilin sa na ajiye wannan mukami, cewar bai amince da aka baiwa Femi Fani kayode sarautar Saukin Shinkafi ba, saboda ya dade yana sukar arewa da shugabanninta.

Ya kara da cewa sarautar Sadauki, sarauta ce mai daraja, wanda duk wanda yake da sarautar zai iya sadaukar da rayuwar sa da dukiyar sa ga al'ummar yankin, da addinin su da al’adun su da zamantakewar su, da kuma kare mutunci da muradun wadannan al’umma.

Mai bada shawara na musamman ga gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Zailani Baffa ya shaidawa wakilin muryar Amurka cewa, gwamnati ba ita take zabar duk wata sarauta ba.

Saurari Karin bayani cikin sauti daga Sani Malumfashi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:53 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG