Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Majalisar Wakilai Sun Ba Gwamnati Shawara a Game da Shugaban INEC


Shugaban hukumar zabe ta Najeriya, Attahiru Jega
Shugaban hukumar zabe ta Najeriya, Attahiru Jega

'Yan majalisar wakilan Najeriya sun jawo hankalin gwamnati

A wata hira da wakilin sashin Hausa Ladan Ayawa yayi da daya daga cikin 'yan majalisar wakilan Najeriya Honourable Musa Ada yace, "a matsayin su na 'yan majalisa sun dauki wannan matakin jawo hankalin gwamnatin kasar ne agame da maganganun da jaridun kasar ke ta yayatwa cewar za'a dakatar da shugaban hukumar zabe Farfesa Attahiru Jega".

Dan majalisar yayi karin bayanin cewa hakan da sukayi sunyi wa kasa adalci ne, sai dai kuma yace akwai bukatar mutane su sani cewar, tun farko anyi kuskuren nada Farfesa Attahiru Jega a matsayin shugaban na INEC saboda kwamitin da marigayi shugabankasa Umar Musa ya kafa ya bada sharuddan da yakamata ayi amfani dasu wajan nadin shugaban hukumar amma shugaban kasa yayi burus da lamarin ba tare da bin ka'idodin kwamitin ba.

"Rashin bin doka da oda shi yasa shugaban kasar ke yin abinda yaga dama, kamar cire Farfesa Moris Iwu wanda ke shgabancin hukumar ba tare da wa'adin shi yayi ba, cire Sanusi Lamido wato tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN ba tare da wa'adin sa yayi ba duk irin wadan nan ke kawo matsaloli makamantan haka". a cewar dan majalisar.

Daga karshe ya bayyana cewar shawara ce suka ba shugaban kasar a matsayin su na masu yin dokar kasa.

ZABEN2015: 'Yan Majalisar Wakilai Sun Ba Gwamnati Shawara a Game da Shugaban INEC - 2'33"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:33 0:00

XS
SM
MD
LG