Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Malawi-Dubban 'Yan Kasar Suka Yi Zanga-zangar Kyamar Cin Hanci Da Rashawa.


Masu zanga zanga kenan akan babbar hanyar da ake kira Kamuz a birnin Blantyre, Malawi, April 27, 2018.
Masu zanga zanga kenan akan babbar hanyar da ake kira Kamuz a birnin Blantyre, Malawi, April 27, 2018.

Domin gudun kada akuma abunda ya faru a shekara ta 2011, titunan birnin Balantyre babu kowa kuma an rufe shaguna a gangamin na jiya dubban 'yan kasar suka yi maci.

A Malawi, dubban 'yan kasar ne suka yi zanga zanga a duk fadin kasar a ranar jumma'a, don nuna rashin amincewar su kan cin hanci da rashawa, da kuma rashin shugabancin ko gwamnati ta kwarai.

Ana zanga zangar kwana daya kamin tsohuwar shugabar kasar Joyce Banda ta koma kasar, bayan ta yi shekaru 4 anan Amurka, ana dai ci gaba da bincike kan zargin cin hanci da rashawa zamanin shugabancinta. Lameck Masina ya aiko mana da rahoto daga birnin Balantyre.

Lameck yace harkokin kasuwanci sun tsaya cik, a babban birnin kasuwanci na kasar a jiya Jumma'a. Inda kusan ba zaka ga kowa akan babban titin birnin na Balantyre ba, yayinda aka rufe kantuna da wasu wuraren kasuwanci.

Mutane masu yawa suna fargabar kada a kuma abunda ya faru lokacin wata zanga zangar nuna kyamar gwamnati, inda aka harbe masu zanga-zanga 20.

Daya daga cikin jagororin shirya shirya zanga-zangar a birnin na Balantyre Masuko Thawe, ya yabawa wadanda suka fito saboda gudanar da zanga-zangar cikin lumana, kuma kamar yadda yace, babu wanda ya jikkata ko aka ketawa yanci.

Masu zanga zangar suna neman shugaban kasar Peter Mutahrika, ya janye nada Rodney Jose, a matsayin mukaddashin speto Janar na 'Yansandan kasar. Ana zargin Jose da hanu a kisan wani dalibin wata jami'a a shekara ta 2011.

Masu zanga-zangar sun kuma bukaci gwamnati ta kawo karshen daukewar wutan lantarki a kasar.

'Yansandan kasar sun ki suce ko zasu kama tsohuwar shugabar kasa Banda, bayan da abun fallasa kan kudi dalar Amurka milyan 32 suka salwanta. Galibin wadanda aka hukunta akan batun kudin duk sun yi zargin cewa itace kanwa uwar gami a wannan badakalar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG