Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Najeriya Milyan 32 Zasu Fuskanci Matsananciyar Yunwa Nan Da Watan Yunin Bana-Rahoto


Kayan abinci
Kayan abinci

A cewar rahoton, adadin mutanen da zasu fuskanci matsalar karancin abinci a yankunan yammaci da tsakiyar nahiyar afirka a wannan dan tsakani zai kai kimanin mutane milyan 52 kwatankwacin kaso 12 cikin 100 na mutanen da aka tantance.

Akwai yiyuwar cewar akalla ‘yan Najeriya miliyan 32 ne zasu fuskanci wani yanayi mai kama da matsananciyar yunwa a tsakanin watanin Yuni da Agustar shekarar da muke ciki matukar ba’a dauki matakan gaggawa ba, a cewar rahoton Cadre Harminise’ na baya-bayan nan, wanda kwamitin kai dauki na kasa da kasa da gwamman kungiyoyin kasa dake aiki a yankin suka wallafa.

A cewar rahoton, adadin mutanen da zasu fuskanci matsalar karancin abinci a yankunan yammaci da tsakiyar nahiyar afirka a wannan dan tsakani zai kai kimanin mutane milyan 52 kwatankwacin kaso 12 cikin 100 na mutanen da aka tantance.

Rahoton ya bayyana cewar, “a bisa tsinkayen da muka yi, abinda ake hasashen zai faru tsakanin watannin Yuni zuwa Agustar shekarar da muke ciki zai ma fi yadda ake tunani tsanani: ana sa ran kimanin mutane milyan 52 daga kasashe 17 da aka nazarta zasu fuskanci gaba ta 3 zuwa ta 5 na wannan lokaci na karancin cimaka tsakanin watan Yuni zuwa Agusta. Hakan na nufin cewar kaso 12 cikin 100 na al’ummar da aka nazarta zasu sha bakar wahala wajen samun abin kaiwa bakin salatinsu.

Kasashen da al’amarin zai shafa sun hadar da Mauritaniya (inda zai shafi mutane 656, 652, kwatankwacin kaso 14 cikin 100) da Burkina Faso (inda zai shafi mutane 2, 734, 196, kwatankwacin kaso 12 cikin 100) da Nijar (inda zai shafi mutane 3, 436, 892, kwatankwacin kaso 13 cikin 100) da Chadi (inda zai shafi mutane 3, 364, 453, kwatankwacin kaso 20 cikin 100) da Saliyo (inda zai shafi mutane 1, 569, 895, kwatankwacin kaso 20 cikin 100) da Najeriya (inda zai shafi mutane 31, 758, 164, kwatankwacin kaso 16 cikin 100).

Har ila yau, rahoton ya kara da cewar matsalar karancin cimakar zata fi kamari a jihohin arewacin Najeriya irinsu Sokoto da Zamfara inda fashin bakin da aka yi ya bayyana yanayin da mai matukar tsanani, harma fiye da kaso 15 cikin 100 na kananan yara zasu yi fama da cutar tamowa da karancin abinci ke haddasawa.

Rahoton na IRC ya alakanta dalilan tsanantar matsalar karancin cimakar a yankin sahel ga matsalolin rashin tsaro da sauyin yanayi da kuma tabarbarewar tattalin arzikin kasashe, musamma ma matsalar hauhawar farashin kayan masarufi.

A watan Janairun daya gabata, yawaitar hauhawar farashin kayan masarufi ta kai kaso 21 cikin 100, inda ya karu daga kaso 18 cikin 100 da aka gani a sjekarar bara. Kasashen da al’amarin yafi kamari ma sune irinsu Saliyo inda hauhawar farashin ta kai har kaso 54 cikin 100

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG