Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Najeriya Na Cigaba Da Kokarin Yin Rajistar Samun Lambar Shaidar Ajiyar Banki


Hedikwatar Babban Bankin Najeriya, Abuja

Yayin da zamantakewa da tattalin arzikin Najeriya ke cigaba da ganin sauye-sauye, ciki har da tsarin rajistar samun lambar shaidar mallakar ajiya a banki, kwararru na cigaba da bayyana muhimmancin wadannan matakan

Yayin da ‘yan Najeriya ke ta kokarin rajistar samun lambar shaidar ajiya a banki ta wajen gabatar da kai da kuma dangwala yatsa (biometric) da sauran matakan da su ka hada da gabatar da wasu takardun shaida, su kuma kwararru sun shiga bayyana ma mutane muhimmancin wannan rajistar.

Wakilin Sashin Hausa Nasiri Adamu Elhikaya ya ce sabanin yadda aka yi ta cika bankuna don neman yin rajistar dab da cikar wa’adin baya, a ‘yan kwanakin an samu cinkoson masu bukatar rajistar amma ba dayawa ba a daidai lokacin da wa’adin 31 ga watan Oktoba ke kara karatowa.

Ya ce rajistar, wadda Babban Bankin Najeriya ya wajebta ga duk masu ajiya a duk wani banki a Najeriya. Da farko wa’adinta ya cilka a karshen wata Yuni, amma ganin mutane da dama sun kasa samun yin rajistar, sai aka tsawaita wa’adin zuwa karshen watan Oktoba. Kuma rahotannin na nuna cewa, wannan karon ma an dage zuwa karshen watan Nuwamba.

Wani Masanin Tattalin Arziki mai suna Hashimu Muhammed ya bayyana ma Nasiru muhimmancin wannan lambar. Ya ce wannan lambar za ta nuna duk wanda ya shigar ko ya fitar da kudi da kuma wanda ya karbi kudin da dai sauran bayanai masu muhimmanci. Y ace daga yanzu ma duk wanda za a saida ma sa kudin waje sai ya nuna lambar. Wani wanda ya yi rajistar mai suna Yusuf Ishaq ya bayyana muhimmancin rajistar da cewa zai taimaka wajen yaki da ta’addanci ganin yadda ‘yan ta’adda me samun kudadensu a boye.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG