Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Nijar Kusan Miliyan Biyu Za Su Amfana Da Ayyukan MDD


Firayim Ministan Nijar, Biriji Rafini

Jakadun Majalisar Dinkin Duniya na yakin Sahel sun gudanar da bikin tsarin jadawalin ayyukan jin-kai da za su yi a Nijar tare da bayyana wadanda za su ci gajiyar ayyukansu.

Jakadun Majalisar Dinkin Duniya na yankin Sahel sun ce mutane kimanin miliyan1.8 ne za su amfana da ayyukan da ke kunshe da wani tsarin samar da ayyuka da suka yi.

Galibin mutanen da ke cikin matsala sun fito ne daga yankunan Diffa da Tilabery, yankunan da suka fi fama da rikicin ta'addanci.

A shirin na Majalisar Dinkin Duniya, yaki da karancin abinci na kan gaba kamar yadda Bintu Jibo shugabar jakadun a Nijar, ta ce.

Ta kara da cewa, baya ga matsalar karancin abinci, shirin zai maida hankali akan cutar tamowa wadda take addabar yara a cikin shirin kiwon lafiya.

Sannan akwai shirin samar da ruwan sha da inganta ilimin yara.

Bayanai na nuni da cewa yawan mutanen davke cikin kangi a bana, ya zarta na 2017 lamarin da Madam Jibo ta ce yana da nasaba da tabartarewar tsaro akan iyakar Burkina Faso da Mali.

Wannan kuma yana shafar jamhuriyar ta Nijar cewarta.

Hukumomin Nijar ta bakin Firai Ministan kasar Birji Rafini yayin kaddamar da tsarin jaddawalin ayyukan jin-kai na Majalisar Dinkin Duniyan, sun bukaci hadin gwuiwa da gwamnati domin tsara fasali daya tilo daga badi.

Saurari rahoton Sule Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:38 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG