Ana ci gaba da musayar kalamai tsakanin jamiyun APC, da PDP mai mulki, inda kowane bangare ke azawa daya bangaren laifin neman kawo tada zaune tsaye a kamfe din da ake yin don zaben watan Fabrairu.
APC, dai wace ta tuno yanda ‘yan sanda suka harbawa kakakin majalisa, Aminu Tambuwal, barkonon tsohuwa, don ya sauya sheka, sun bukaci sako wasu ‘yan adawa, da jami’an tsaro suka kama, a Gombe, biyo bayan tarzoman matasa, da suka jefi ayarin motocin Gwamna Hassan Dankwambo, a garin Kashere.
Sai dai nan take jami’in, labarum Gwamnan, Junaidu Muhammad, yace ‘yan adawa, sun kai hari ne don hallaka Gwamnan.
Dan takaran Gwamnan Jihar ta Gombe, a inuwar jamiyar APC, Mahamud Inuwa Yahaya, ya musanta, wannan ikirarin, ya kuma kara da cewa idan ‘yan sanda sun kamasu inna hujja nacewa akwai wani makami, da aka yi amfani dashi.