Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Republican Masu Neman Shugabancin Amurka Sunyi Muhawara A Iowa


Shugaban Jam'iyyar Republican na ksa Reince Priebus

‘Yan takarar shugabancin Amurka a tutar Republican sunyi muhawara a jihar IOWA dake tsakiyar Amurka, da nufin tsuma magoya bayansu, gabannin gudanar da zabe na gwaji a jihar ta IOWa

‘Yan takarar shugabancin Amurka a tutar Republican sunyi muhawara a jihar Iowa dake tsakiyar Amurka, da nufin tsuma magoya bayansu, gabannin gudanar da zabe na gwaji a jihar ta IOWa, domin gano wadanda suka fi karfi da karbuwa a zaben share fage, a zaben shugaban kasa da za a yi badi.

‘Yan takara takwas ne suka kara a muharawar da aka nuna kai tsaye ta talabijin daga harabar jami’ar Iowa dake birnin Ames.

‘Yan takarar sun hada da tsohon gwamnan Massachussetts Mitt Romney, wanda yake kan gaba ahalin yanzu, ‘yar majalisar wakilai ta tarayya Michelle Bachman, kuma shugabar ‘yan rikau reshen Tea Party a majalisar.

Haka kuma cikin wadanda suka shiga muhawarar har da tsohon Gwamnan Minnesota Tim Pawlenty, da kuma wakili a majalisar wakilai Ron Paul, da kuma tsohon jakadan Amurka a China Jon Huntsman. Da kuma wani bakar fata dan kasuwa.

Mutuminda bai shiga muhawarar ba shine Gwamnan jihar Texas Rick Perry, wadda ake sa ran zan bayyana niyyar takarar shugabancin Amurkan gobe Asabar idan Allah ya kaimu.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG