Majalisar ta gayyaci Comey ne ya bayyana gaban kwamitin da yake sa ido kan yadda bangaren zartaswa yake tafiyarda ayykansa, yayinda Ministan shari'a kuma Atoni Janar ta Amurka Loretta Lynch zata bayyana gaban kwamitin majalisar mai kula da harkokin shari'a. Zata bayyana gaban kwamitin ne makon gobe.
Lynch da kuma Comey sun gana jiya Laraba, gabannin ya bayyana gaban kwamitin. Atoni Janar Lynch dai tace zata mutunta shawarar da hukumar FBI ta bayar kan wannan batu.
Kakakin majalisar wakilai Paul Ryan ya fada jiya Laraba cewa, ta yiwu an yiwa Mrs Clinton gata a binciken da aka yiwa tsohuwar babbar jakadiyar Amurkan. "Da akwai alamun haka a ganina," kakakin ya gayawa manema labarai jiya Laraba.