Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sandan Najeriya Sun Yi Karin Haske Kan Harin Maiduguri


Wani yanki a Maiduguri da rikicin Boko Haram ya shafa

Bayan wani hari da wasu 'yan kunar bakin wake suka kai a Maiduguri dake jihar Bornon Najeriya dake arewa maso gabashin kasar, hukumomin tsaro sun fayyace adadin mutanen da suka mutu ya zuwa yanzu.

'Yan sanda sun fada a jiya Laraba cewar akalla mutane 17 aka kashe a wasu jerin hare- hare a arewa maso gabashin Najeriya.

'Yan harin kunar bakin wake guda hudu ne a cewar 'yan sandan suka kai hare-haren a birnin Maiduguri a daren shekaran jiya Talata inda suka raunata sama da mutane 20.

Rahotannin farko sun bayyana cewa mutane 19 ne suka mutu

Galibin wadanda hare haren ya rusa da su 'yan tsaron farin kaya da aka fi sani da "Civilian JTF" da suka kafa shingaye a cewar 'yan sandan cikin gida.

Harin na ranar Talata shi ne mafi muni da birnin ya gani tsakanin 'yan watannin nan.

Facebook Forum

Shugaba Joe Biden ya zama Shugaban Amurka na 46

Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris

BIDIYO: Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:51 0:00

An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris

BIDIYO: An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46
please wait

No media source currently available

0:00 1:45:22 0:00
XS
SM
MD
LG