Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Sanda Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane A Jihar Nassarawa


Masu Garkuwa Da Mutane
Masu Garkuwa Da Mutane

Rundunar ‘yan sandan Jahar Nasarawa a arewacin Najeriya ta yi nasarar kama mutane goma sha bakwai da ake zargi da ayukan garkuwa da mutane don karbar kudin fansa.

An sami kama wadanda zargin da garkuwa da mutane ne a ayukan sintiri da samame da ‘yan sanda suka yi tun daga watan Fabrairu zuwa watan Afrilun wannan shekara ta 2023, a cewar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa, DSP Ramhan Nansel.

DSP Ramhan Nansel yace a yayin gudanar da aikin na su, sun kuma yi nasarar kubutar da mutane biyar da aka yi garkuwa da su, tare da kwace bindigogi hudu da albarusai takwas daga masu wadanda ake zargin.

Masu Garkuwa Da Mutane
Masu Garkuwa Da Mutane

Ya kara da cewa binciken da suka gudanar ya nuna cewa wadanda aka kama, suna tare babbar hanyar Nasarawa Eggon zuwa Akwanga da ma cikin garin Lafia da kewaye zuwa kudancin jihar ta Nasarawa, inda kuma suke sace mutane.

A makon da ya gabata ne tsohon mataimakin gwamnan jihar Nasarawa, Farfesa Onje Gye Wado ya kubuta a hannun wadansu da suka yi garkuwa dashi.

A wata tattaunawa da shi, tsohon mataimakin gwamnan ya bayyana cewa wadanda suka yi garkuwa da shi matasa ne da ke sana’ar kiwon dabbobi, don haka ba ya zaton talauci ne ko rashin aikin yi ya sanyasu shiga sha’anin garkuwa da mutane.

Masu Garkuwa Da Mutane
Masu Garkuwa Da Mutane

Dakta Mukhtar Wakeel mai sharhi kan lamuran yau da kullum ya ce son zuciya ne ke sanya mutane aikata miyagun laifuka.

Rundunar ‘yan sandan ta jihar Nasarawa ta kuma sha alwashin hada kai da sauran jami’an tsaro don kakkabe bata gari a Jahar.

Saurari sautin rahoton Zainab Babaji:

'Yan Sanda Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane A Nassarawa
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

XS
SM
MD
LG