Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Tasa Keyar Wasu Matasa


Rundunar ‘yan Sandan jihar Legas ta cafke wani matashi mai gadi mai suna Bala Usman, wanda ake zargi da hada baki domin yiwa mai gidansa sata.

Shi dai Bala Usman, ana zargin cewa ya sace mukullin motar mai gidansa kirar Honda, ya kuma gayyaci abokansa, Chika Asogwa da Abubakar Garba, cewa su tsere da motar.

Jami’an ‘yan Sandan unguwar Isolo, ne suka cafke Bala Usman, da abokansa a daidai lokacin da suke kokarin sayarda motar, akan kudin Nairamiliyan biyu, a maimakon Naira miliyan shida.

Da yake tabbatar da lamarin kakakin ‘yan Sandan jihar ta Legas SP Dolapo Badmos, yace motar miliyan shida da suke bukatar sayarda shi akan miliyan biyu ya jawo zargi daga masu sayen motar.

Banda su ukku, akwai wasu mutane biyu Chike Umeh da Ekene Eze, da suma suna hannun ‘yan Sanda saboda su suka taimaka masu wajan tallatar da motar.

Kakakin ya kara da cewa da zarar an kammala bincike za’a gurfanar dasu a kotu domin yi masu sharer kamar yadda doka ta tanada.

XS
SM
MD
LG