Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Sandan Jihar Texas Na Fuskantar Tambayoyi Masu Tsauri Kan Kisan Mutane 21


Harbin Makaranta a Texas
Harbin Makaranta a Texas

Dan bindigar da ya kashe mutane 21 ya shafe sa'a guda a makarantar firamare ta Robb kafin 'yan sanda su harbe shi

Hukumomin tsaro a jihar Texas da ke kudu maso yammacin Amurka na fuskantar tambayoyi masu tsauri game da martanin da suka mayar da kuma tsawon lokacin da suka dauka a wannan makon kafin su kutsa kai a wata makaranta domin tinkarar wani matashin dan bindiga da ya harbe har lahira yara 19 da malamai 2.

Jami’a sun ce dan bindigar mai suna Salvador Ramos, matashi ne dan shekara 18 da ya bar makarantar sakandare, ya shafe mintuna 40 zuwa sa’a daya a makarantar, kafin ‘yan sanda su kutsa cikin aji hudu, inda ya kashe mutane 21 a makarantar firamare ta Robb da ke karamin garin Uvalde a jihar Texas.

Shaidu sun ce iyayen yaran da suka makale a makarantar da ke kusa da unguwar da suke zaune, kuma ‘yan kallo da suka taru da tsakar ranar Talata, sun dagawa ‘yan sanda murya da su shiga makarantar su kawo karshen barna.

Wani da ya shaida lamarin a wajen makarantar, Juan Caranza, mai shekara 24, wanda ya kalli abin da ya faru daga wajen gidansa da ke kan titi, yace mata sun dagawa ‘yan sanda murya, “Ku shiga ciki! Ku shiga ciki!”

XS
SM
MD
LG