Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Shi'a Sun Bukaci a Soke Jam'iyyar APC


Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, shugaban kungiyar Shi'a a Najeriya
Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, shugaban kungiyar Shi'a a Najeriya

Sanadiyar kin bin umurnin kotu akan sakin shugaban Shi'a Sheikh El-Zakzaky da gwamnatin tarayya ta yi, mabiya darikar a jihar Filato sun yi kira ga hukumar zabe da ta soke rijistar APC. Sai dai a martaninta, jam'iyyar ta APC, ta ce wannan ba batu ba ne na jam'iyya.

Mabiya mazahabr Shi'a a Najeriya sun yi kira ga hukumar zaben kasar, wato,INEC da ta soke rajistar jam'iyyar APC mai mulki.

Reshen kungiyar na jihar Filato ne ya yi wannan kira bisa dalilin cewa gwamnatin APC ta ki bin umurnin kotu, wacce ta yanke hukuncin a saki El-Zakzaky.

Daya daga cikin almajiran Sheikh El-Zakzaky Nura Waziri a Jos a wani taron manema labarai ya bayyana cewa sun rubutawa hukumar zabe akan bukatarsu idan kuma ba ta dauki mataki ba za su garzaya kotu.

A cewarsa, tun a watan Disamban bara kotu ta ba da umurnin a saki shugabansu a kuma biya shi diyya, sannan a mayar masa da gidansa kana a bashi tsaro.

Amma duk hakan ya cutura a cewar Waziri.

Sai dai a martanin da ya mayar, mataimakin shugaban jam'iyyar APC na yankin arewa ta tsakiya, Alhaji Zakari Abdullahi Idi, ya ce an yi rajistan APC a karkashin doka ne idan kuma ta sabawa dokar ba mabiya Shi'a ne za su ce a janye rajistarta ba.

Wannan hurumi ne na hukumar zabe INEC inji Idi.

Saurari rahoton Zainab Babaji domin karin bayani:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:18 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG