Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Ta'adda Da Ke Rike Da Wasu 'Yan Mata 'Ya'yan Tsohon Akanta-Janar Na Zamfara Sun Yi Barazanar Tilasta Su Aikin Ta’addanci


DIG Usman Alkali Baba
DIG Usman Alkali Baba

A wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, wasu 'yan ta'adda sun yi barazanar tilasta wasu 'yan mata biyu 'ya'yan tsohon Akanta-Janar na Zamfara yin aikin ta'addanci tare da su.

‘Yan ta’addan da ke rike da wasu 'yan mata biyu ‘ya’yan tsohon Akanta-Janar din Jihar Zamfara, Abubakar Bala Furfuri, da wata ma’aikaciyar gidansa, sun yi barazanar mayar da su ’yan ta’adda.

Sun yi kashedin cewa idan su ka mayar da yaran 'yan ta'adda, za su yi amfani da su wajen jawo hankalin sauran masu aikata muggan laifuka idan iyayen yaran suka kasa biyan kudin fansa da suka nema.

Sakon 'yan ta'addar na kunshe ne a cikin wani faifan bidiyo na mintuna 2:39 da aka fitar da safiyar Litinin wanda kuma har yanzu ke yawo a kafafen sada zumunta.

Yaran, Zulaihat da Zainab da wata ma’aikaciyar gida da ba a bayyana sunanta ba, sun shafe kwanaki 128 a hannunsu. A watan Yuni ne aka sace su. A cikin faifan bidiyon, an ga matan uku rike da bindigogin kakkabo jiragen sama, AK 47, LMG da sauran bindigogi.

Bidiyon ya fara ne da daya daga cikin 'yan ta'addan da ke baya can yana gaya wa 'yan matan (cewa sun yi biyon ne) saboda iyayensu "suna tunanin batun wargi ne ko kuma karya." Sai kuma ya ce “Ba ma kudin ne ya dame mu ba. Za mu yi amfani da ku ne kawai mu ƙara yawan mayakanmu ko kuma mu yi amfani da ku wajen auna wasu wurare. "

Wani kuma ya katse shi ya ce, "ku gaya musu idan ba su bamu hadin kai ba, za mu ci gaba da tozarta su."

- Premium Times

XS
SM
MD
LG