Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Takarar Shugaban Kasa a Najeriya Na Ci Gaba Da Yakin Neman Zabe


A ci gaba da gangamin neman kuri'u da yan takara ke yi a Najeriya, Shugaba Buhari na jam'iyyar APC ya kai ziyara jihar Taraba dake fama da matsalar tsaro a arewa maso gabashin kasar, inda ya ce, APC ita zata kafa gwamnati a Taraba wannan karon.

Kamar dai yadda aka gudanar da gangamin jam'iyyar, PDP daruruwan jama'a ne suka halarci gangamin na APC da aka yi a filin wasan Stadium dake Jalingo inda kusoshin jam'iyyar suka baje kolinsu.

Tun farko a jawabin sa shugaban jam'iyyar APC Adams Oshomole shagube yayi, ga babbar jam'iyar adawa inda ya ce zasu cika alkawuran da suka yiwa 'yan Najeriya.

Wannan ziyarar shugaban kasar ita ta kawo karshen cece-kucen da ake yi na batun takarar gwamnan jihar Taraban, inda aka daga hannun Dan takarar jam'iyyar Sani Abubakar Danladi, Wanda ya nuna farin cikin sa.

To sai dai kuma a jawabin sa shugaba Buhari wanda ya nuna damuwarsa game da wasu matsaloli dake addabar kasar, ya ce gwamnatin sa ta kawo sauyi a Najeriya, ba kamar yadda 'yan adawa ke zargi ba.

Sakamakon tattaruwar da jama'a suka yi, an sami turmitsitsi har wasu suka samu raunuka, koda yake kawo yanzu babu tabbacin ko an samu hasarar rai ko kuma a'a.

Ga karin bayani cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:24 0:00

Facebook Forum

Ana ci gaba da muhawara a kan ko daga wane yanki na Najeriya yakamata shugaban kasar na gaba ya fito

Karin bayani akan Bidiyo

Sabbin kotunan soji a Maiduguri za su yi shari’a ga kanana da manyan sojoji

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zabarmawa, Zabuwa, Ghana

Yadda Aka Gudanar Da Wasan Zabuwa A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Aminu Saira

Aminu Saira
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:04:33 0:00
Karin bayani akan Nishadi
XS
SM
MD
LG