Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan tawaye a Syria sun kauracewa zaben Majalisar dokoki


Wata mace ke fitowa bayan tayi zabe Litinin din nan a birnin Damascus

Masu gwagwarmaya a Syria sunce yan tawaye a birane da kauyuka da dama sun kauracewa zaben wakilan Majalisar wakilan da kungiyoyin yan tawaye suka baiyana zaman soki burutsu.

Masu gwagwarmaya a kasar Syria sunce masu yiwa gwamnatin Syria bore a kauyaka da birane da dama su kauracewa zaben wakilan Majalisar dokoki, da manyan kungiyoyin masu hamaiya suka baiyana a zaman soki burutsu ne kawai.

Masu gwagwarmaya sunce tituna fayau suke, kuma an rufe kantuna a birnin Hama da wasu birane inda masu hamaiya suke da karfi, a yayinda mazauna biranen suka shiga yajin aiki a yau litinin domin nuna rashin amincewarsu ga zaben da ake yi yau litinin.

Gudanar da zaben shine yunkuri na baya bayan nan da gwamnatin Syria ta shugaba Bashar Al Assad tayi domin nuna cewa ana gudanar da sauye sauyen democradiya a kasar, kasar da tun shekaru alif dari tara da saba'in danginsa ke jan ragamar mulkin kasar.

To amma kuma sanannun kungiyoyin masu hamaiya a ciki da wajen kasar sun baiyana cewa zaben shirme ne kurum da ba za'a mutunta sakamakonsa ba, domin sojoin Assad suna ci gaba da murkushe masu hamaiya da karfi tsiya.

Gidan talibijin na Syria ya nuna mutane suka kada kuri'unsu a Damascus baban birnin kasar da wasu wurare. Yan tara dubu bakwai ne ke takarar kujeru maitan da hamsi da Majalisar dokokin kasar.

Wasu masu kada kuri'a a Damascus sunce, suna da alhakin jefa kuri'a, wasu kuma sun baiyana fatar samun canji.

Mai magana da yawur masu hamaiya Bassma Kodmani ta fadawa Muryar Amirka cewa gwamnatin Syria ce ta matsawa mutane ala tilas yin zabe a wuraren da suke karkashinta ta hanyar amfani da jami'an tsaro wajen jigilar jama'a zuwa rumfunan zabe.

XS
SM
MD
LG