Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Myanmar 'Yan Tawaye Sun Kashe Akalla Mutane 15 Wasu 20 Sun Jikkata


'Yan tawaye a yankin Kachin na Myanmar da suke fafatawar neman 'yanci.

A Myanamar wata kungiyar 'yan tawaye sun kaddamar da wani hari kan sojojin kasar jiya Asabar a wani gari dake arewacin kasar,suka kashe akalla mutane 15 suka jikkata mutum 20, ciki harda farar hula, kamar yadda jami'an kasar suka ce.

A Myanamar wata kungiyar 'yan tawaye sun kaddamar da wani hari kan sojojin kasar jiya Asabar a wani gari dake arewacin kasar, suka kashe akalla mutane 15 suka jikkata mutum ashirin, ciki harda farar hula, kamar yadda jami'an kasar suka ce.
Kungiyar da ake kira Tang National Libration Army, ko TNLA a takaice, ta kaddamar hare hare har uku da ssubahin jiya Asabar a garin da ake kira Muse a jahar shan, kamar yadda kakakin gwamnati kasar ya fada ta shafin ta a Face book. Biyu daga cikin hare haren an kai su ne kan sansanin sojoji, dayan kuma a kan wata gada.

Kungiyar TNLA tana daga cikin kungiyoyi fiyeda dozen daya da suke fafatawa da gwamnatin kasar domin samun karin 'yanci.

Ana sukar sojojin Myanmar da zartas da yanke hukunci ba da yawun alkali ba, da gallazawa,tilastawa mutane aiki tamkar bayi, da fyade,da wasu cin zarafi kan tsirarun kasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG