Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawayen Houthi Sun Sako Wasu da Suke Garkuwa Dasu


Mayakan Houthi

'Yan tawayen Houthi da suka yi garkuwa da wasu 'yan kasashen waje da suka hada da Amurkawa biyu sun sakosu

Jiya Lahadi suka sako mutanen bayan tattaunawar bayan fagge tsakanin 'yan tawayen da gwamnatin Oman wadda ta wakilci kasashen mutanen.

Babu wani cikakken bayani da aka bayar dangane da sako mutanen kuma babu wanda ya san tabbas abun da aka cimma.

Kawo yanzu ba'a tantance wadanda aka sakon ba. To amma wani kamfani dake da hekwatarsa a New Orleans mai suna Transoceanic Development dake taimakawa da raba kayan agaji yace akwai ma'aikacinsa cikin wadanda aka sako mai suna Scott Darden..

Fadar White House ta bakin mai magana da yawunta Ned Price yace ta godewa duk wadanda suka taka rawa wurin ganin cewa an sako wadanda aka yi garkuwa dasu musamman shugaban Oman Sultan Qaboos bin Said al-Said.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG