Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan tawayen Libya sun kaddamar da harin farko akan birnin Tripoli

Libyan rebels attack government positions near Tripoli.

‘Yan tawayen Libya sunce jiya asabar da dare suka kaddamar da harinsu na farko akan Tripoli baban birnin kasar tare da agazawar sojojin kungiyar kawancen tsaro ta NATO, abinda suke fatar zata zama danawa ta karshe zuwa birnin, a boren watanin shidda da suke yiwa shugaba Gaddafi.

Tashe tashen bamai bamai da karajin harbe harbbe sun girgiza birnin Tripoli a cikin dare a yayinda gwamnatin kasar ta musunta cewa ana hargitsi a birnin. Mai magana da yawun gwamnati Moussa Ibrahim yace wasu kungiyoyin yan tawaye dauke da makamai ne suka kutsa cikin birnin, amma yace nan da nan aka murkushe su.

A wani sakon vidiyo da aka nuna ta gidan talibijin na kasar, shugaba Gaddafi yayi watsi da ikirarin yan tawayen akan cewa yunkuri ne kawai na wadanda ya kira maciya amana kasa da beraye suka yi.

An samu rahotanin cewa ana fafatawa a birnin Tripoli sa’o’i bayan da aka bada rahoton cewa yan tawaye sun mamaye birane masu muhimmanci guda biyu da suka hada harda Zawiya a yammacin kasar da kuma Brega a gabashin kasar. A Zawiya yan tawaye snce yanzu sune ke iko da sansanonin da da suke hannun sojojin Gaddafi wadanda suka ci gaba da yiwa birnin luguden wuta daga gabashi. Haka kuma wani baban kwamandan yan tawaye ya fada a jiya asabar cewa mayakansa sune ke iko da birnin Brega. Ba’a dai tabbatar da wannan ikirari daga wata kafa ta fisabillilahi ba.

XS
SM
MD
LG