Accessibility links

'Yan Tawayen Kungiyar M23 Sun Janye Daga Birnin Goma Zuwa Wani Wuri Mai......

  • Aliyu Imam

'Yan tawayen M23 sukwe zaune cikin wata mota lokacinda suke shirin janyewa daga wani gari dake gabashin kasar.

‘Yan tawaye a jamhuriyar demokuradiyyar kwango da ake kiyasin yawansu ya kai dari ukun sun janye daga birnin Goma dake gabashin kasar, wuri mai muhimmanci sabo da ma’adinai da ake haka, da dakarun suka kama mako biyu da suka wuce.

Wakilin Muriyar Amurka Gabe Joselow, ya aiko da rahoto daga Goma cewa, ‘yan tawayen sun doshi arewa, suka girke kansu a wuri mai tazarar kilomita 20 daga birnin, karkashin yarjejeniyar da aka kulla, da kasashe dake yankin suka shiga tsakani.

Kakakin masu aikin kiyaye zaman lafiya na MDD Kieran Dwyer, yayi marhabin da janyewar, duk da haka yana gargadin cewa janyewar matakin farko ne domin har yanzu zaman lafiya bai kankama ba sosai a yankin. Yace yana da muhimmancin gaske kungioyar ‘yan tawaye ta M23 ta mutunta sharuddan janyewar, yayinda ake aiki domin samo hanyoyin warware wannan rikici mai dorewa.

Ana sa bangaren shugavban ‘yan tawayen Sultani Makenga yayi kashedi jiya Asabar cewa a shirye dakarunsa suke su sake dawowa birnin idan shugaba Kabila bai mutunta yarjejeniyar janyewar ba.

Galibin wadanda suke cikin kungiyar ta M23 ‘yan tawayene da aka saka su cikin rundunar sojojin kasar, kamin su bijire a farkon shekaran nan, kan zargin ana nuna musu wariya da kuma kuntatawa.
Kungiyar ta lashi takobin sai ta hmabare shugaba Joseph kabila, wanda suke dauka cewa ba halattacce bane.

Ahalinda ake ciki kuma, masu aikin ceto a jamhuriyar demokuradiyyar kwangon sun ce akalla mutane 30 ne suka halaka, sakamakon hadarin wani jirgin dakon kaya da ya kaucewa hanyar saukarsa, ya fada cikin gidajen kwana da suke kusa da filin saukar jiragen saman kasar dake Barazzaville, babban birnin kasar, ranar jumma’a da ta shige.
Jirgin dakon kaya da yayi hadari a Barazzaville.
Jirgin dakon kaya da yayi hadari a Barazzaville.

Ma’aikatan jikin su shida, suna daga cikin wadanda hadarin ya rutsa da su, da kuma wasu a kasa da jirgin ya biya ta kansu.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Armenia, ta tabbatar jiya Asabar cewa matuka jirgin ‘yan kasarta ne.
Babu wanin bayani daga hukumomin kasar kan musabbabin hadarin. Amma shaidun gani da ido, sun bada labarin cewa jirgin yayi kokarin sauka ne lokacinda ake ruwa da iska mai karfin gaske.
Jirgin ya taso ne daga birnin Pointe Noire dake yammaci.
XS
SM
MD
LG