Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawayen Sudan Na So a Fara Cudanya


Shugaba Salva Kiir
Shugaba Salva Kiir

A wani al'amari mai kama da yinkurin kawo karshen yakin Sudan Ta Kudu, 'yan tawayen Sudan ta Kudu na kira ga masu ruwa da tsaki da su matsa ma Shugaba Salva Kiir ya saki kudi a yi aikin sasantawa.

Babbar kungiyar ‘yan tawayen Sudan Ta Kudu ta yi kira ga Shugaba Salva Kiir da ya samar da kudi don aiwatar da yarjajjeniyar zaman lafiya da aka cimma bara, su na masu kira ga Sudan da kuma Uganda da su matsa lamba ma Shugaba kiir don ya saki kudin.

Gwamnati da kuma kungiyar ‘yan tawayen SPLM-IO sun rattaba hannu kan yarjajjeniyar don kawo karshen yakin basasar Sudan a ranar 12 ga watan Satumba a Addis Ababa.

Matainakin Ciyaman din SPLM-IO, Henry Odwor, ya ce bangarorin sun makara sosai wajen aiwatar da muhimman fanni na yarjajeniyar, ciki har da mai da sojojin ‘yan tawayen na gwamnati.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG