Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan tawayen Sudan su harbo wani jirgin saman soja


Irin mutane Sudan da suka rasa matsuguninsu a sakamakon fafatawa a kasar.
Irin mutane Sudan da suka rasa matsuguninsu a sakamakon fafatawa a kasar.

'Yan tawayen Sudan sunce su kakkabo wani jirgin saman soja mai saukar angulu suka kashe sojojin gwamnati ashirin da shidda.

'Yan tawayen Sudan sunce sun kakkabo wani jirgin saman soja mai saukar angulu, suka kashe sojoji ashirin da shidda a fafatwar da suka yi a jihar Bule Nile dake kudancin kasar.

Mai magana da yawun kungiyar yan tawaye ta Sudan Peoples Liberation Movement yace a farkon wannan makon aka yi arangamomin a kusa da baban birnin jihar Ed Damazin.

Jami'an soja sun munsunta cewa yan tawaye sun harbo daya daga cikin jiragen samanta mai saukar angulu. Sun baiyana sojojin sun kashe yan tawaye bakwai kuma sojoji shidda ne suka ji rauni.

A watan satumba fada ya barke tsakanin sojojin Sudan da dakarun kungiyar yan tawayen SPLM, wadda ta goyi bayan kudancin Sudan a lokacinda suka fafata yakin basasa.

Majalisar Dinkin Duniya tace fafatawar da ake su sun sa mutane dubu dari arcewa daga gidajensu.

XS
SM
MD
LG