Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawayen Ukraine Sun Yi Bikin Samun Galaba


'Yan Tawaye cikin jerin gwanon motocin yaki suna barin filin daga bayan galabar da suka samu

Bayan sun yi watsi da yarjejeniyar tsagaita wuta da suka cimma 'yan tawayen Ukraine sun yi bikin samun galaba akan dakarun kasar.

A Ukraine 'yan tawaye a gabashin kasar wadanda suke samun goyon bayan Rasha sun gudanar da paretin murna galaba da suka samu kan sojojin Ukraine a Debeltseve da gangami a birnin Donetsk dake kusa. Bukuwan da suka yi a birnin da galibin jama'arta masu magana ne da harshen Rasha yana zuwa ne a dai dai lokacin da gwamnatin dake Kyiv ta roki kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya tura sojojin kiyaye zaman lafiya a yankin kasar da yaki ya daidaita.

Macin da aka yi a Donestk ranar hutu ce a Rasha da kuma wasu sassan tsohuwar tarayyar Soviet, ranar da ake mutuntawa a zaman lokacin karrama masu kare kasa. Wasu rahotanni daga yankin sun hada harda hotunan samun Firayim Ministan yankin Crimea da aka nada wanda aka ganshi yana kada bindigar AK47 a birnin Simferopol, da kuma hoton wani yaro dake murmushi akan wani jirgin yakin Rasha yana gaisuwa irin ta soja a tashar jiragen ruwa dake Sevastopol a yankin na Crimea.

A yayinda ake haka, ministan harkokin wajen Ukraine, Pavlo Kilmkin ya roki wakilan kwamitin sulhu su 15 baki dayansu cewa ya tura sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa gabashin Ukraine.. Mr. Klimkin ya zargi Rasha da 'yan tawaye da take marawa baya da yin watsi da jarjejeniyar tsagaita wuta da aka amince a Belarus ranar 12 ga wannan watan.

XS
SM
MD
LG