Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Togo Na Zanga-zanga Kan Babakere A Mulki


Wani bangare na masu zanga-zanga a Togo
Wani bangare na masu zanga-zanga a Togo

A cigaba da bijire ma shugabannin Afirka da ke son tabbata bisa mulki, 'yan ksar Togo sun bazu bisa titunan Lome don nuna rashin amincewa da kane-kanen da iyalan Gnassingbe ke a a shugabancin kasar.

An katse layukan hanyoyin sadarwar 'intanet' a Togo a jiya Alhamis yayin da hukumomi ke shirin tinkarar zanga-zanga a rana ta biyu, ta bukatar kawo karshen babakeren mulki na tsawon shekaru 50 da Shugaba Faure Gnassingbe da iyalansa ke yi.

Dubun dubatan mutane, bisa jagorancin shugabannin jam'iyyun adawa na Togo, sun mamaye titunan Lome, babban birnin kasar da kuma wasu biranen kasar da dama su na ta kira ga Shugaba Gnassingbe da ya sauka muddun wa'adinsa ya kare a shekarar 2020, a kuma yi garanbawul ga kundin tsarin mulkin kasar don a shigar da kayyadadden wa'adi. A shekarar 1992 aka kafa dokar da ta kayyade wa'adin mulki zuwa sau biyu, to amma sai mahaifin Gnassingbe, marigayi Shugaba Gnassingbe Eyadema, ya soke dokar wa'adin.

Faure Gnassingbe ya zama Shugaban Togo bayan da mahaifinsa ya mutu a 2005, bayan ya shafe shekaru 38 bisa gadon mulki. Ranar Talata Majalisar Ministocin wannan gwamnatin ta amince da wani shiri na maido da kayyadadden wa'adin Shugaban kasa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG