Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yanbindiga Sun Sace Wani Dan Majalisar Dokokin Jihar Bauchi


Jami'an tsaro

Yayin da jam'an tsaro ke fafitikar neman ma'aikacin kiwon lafiya da aka sace sai gashi an sake sace wani da majalisar jihar Bauchi

Satar wasu ma'aikatan kiwon lafiya a Bauchi ya sa jami'an tsaro sun shiga nemansu har sun sami biyu amma kuma a jiya Litinin wasu 'yanbindiga sun sake sace wani dan majalisar dokokin jihar.

Yahaya Muhammed Miya kakakin majalisar dokokin ya bayyana cewa an sace dan majalisar kuma duk matakan da yakama su dauka sun dauka da fatan cewa idan Allah Ya yadda za'a kubutoshi daga hannun mutanen. Ita ma uwargidan dan majalisan da aka sace ta yi bayani. Matar Suwaiba Yusuf Nuhu tace jiya Litinin da magaruba maigidanta ya yi salla ya shiga Masallaci sai wasu dauke da bindigogi suka tsaya bakin gidansu wasu kuma suka shiga masallacin idan yake salla suka daukeshi. Daga nan suka sashi a mota suka tafi dashi. Kawo yanzu babu labarin inda yake.

An sanarda 'yansanda lamarin. Kan ma'aikatan kiwon lafiya da aka sace kakakin 'yansandan jihar Bauchi DSP Haruna Mohammed yace an sako biyu , namuji daya da mace daya amma sauran dayan yana hannun wadanda suka sacesu. Lamarin da ya kawo mutane biyu ke nan a hannun wadanda suka sacesu.

'Yansanda na cigaba da nemansu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG