Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yanke Hukumci Ya Kawo KarshenTakaddamar

Malaysia
Malaysia
Kotun kolin kasar Malaysia ta tabbatar da matakin gwamnatin kasar na haramtawa wata jaridar Roman Katolika yin amfani da kalmar "ALLAH" ta na maganar Ubangijin da suka yi ban gaskiya da shi.

A yau litinin kotun kolin ta yanke hukuncin cewa jaridar The Herald, wadda Majami'ar Roman Katolika ke bugawa da harshen Malay ba ta da hurumin daukaka kara game da hukuncin da wata karamar kotu ta yanke a bara cewa Musulmi ne kawai ya kamata su yi amfani da kalmar "ALLAH", saboda idan wasu addinai suka yi amfani da kalmar, hakan na iya daburta Musulmi, ya ruda su, ya kai su ga yin ridda.

Hukuncin da kotun kolin ta yanke a yau Litinin ya kawo karshen takaddamar da ake yi tun shekarar dubu biyu da bakwai lokacin da ma'aikatar harakokin cikin gidan kasar Malaysia ta yi barazanar kwace lasisin wallafa jaridar The Herald saboda ta na yin amfani da kalmar Larabci a cikin abun da take bugawa da harshen Malay.

A cikin jama'ar kasar Malaysia miliyan talatin, fiye da kashi sittin cikin dari Musulmi ne. Kashi tara cikin dari ne kawai mabiya addinin Kirista a kasar.
XS
SM
MD
LG