Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Binidga Sun Halaka 'Yansanda 54 a Masar.


Al-Wahat Al-Bahriya, yankinda aka yiwa jami'an kwanton bauna.

Jami'an kasar suka ce kwanton bauna ne aka yiwa jami'an lokacinda suka kai somame a yankin hamadar kasar.

Akalla 'Yansandan Msar 54 ne aka kashe a lokacinda suka kai wani somame a maboyar mayakan sakai kusa da birnin Alkahira, kamar yadda jami'an tsaron kasr suka yi bayani.

Jami'an wadanda suka nemi a sakaye sunayensu sun ce an yiwa jami'an tsaron kwanton bauna nea daren jiya jumma'a, bayan suka hallara a mafakar 'yan binidgar dake yankin hamada dake yammacin kasar da ake kira al-Bahriya.

Jami'ai 20 da kuma kurata 34 suna daga cikin wadanda suka halaka a harin. Ma'aikatar harkokin cikin gida a sanarwar da ta bayar tace wasu jami'anta sun yi shahada, sai dai bata bada karin bayani ba

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG