Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yansanda Sun Kama Kwamandan Kungiyar Sa Kai ko Peace Corps


IBRAHIM K. IDRIS, babban sifeton 'yansandan Najeriya

Jami'an yansanda da sojoji da yansandan farin kaya suka kai samame a hedkwar Kungiyar Sa Kai ko Peace Corps a turance inda suka kama kwamandan Mr. Akoh Dickson da sauran mukarrabansa

Kakakin rundunar 'yansandan Najeriya CSP G.O. Moshud bayyana dalilin da ya sa suka kai samamen.

CSP Moshud yana mai cewa kungiyar bata da ikon ta sanyawa jami'anta kayan sarki tare da anfani da baji irin na 'yansanda ko kuma raba 'ya'yanta zuwa yin sintri a wurare daban daban kamar yadda 'yansanda keyi.

Ya cigaba da cewa karambani ne su dinga aiki kaman 'yansanda suna anfani da duka ire-iren kayansu, wato kayan 'yansanda, misali lambobin girma da suke sawa a kafadarsu.

Bugu da kari binciken da 'yansanda suka ce sun gudanar wai har kudi kungiyar ke karba daga matasan dake son shiganta.

To saidai kwamandan kungiyar yace 'yansandan ba gaskiya suke fada ba.Yace dokar da ta basu dama ta bayyana kungiyar a matsayin mungiyar tsaro ta sa kai.

Yanzu dai jami'an 'yansanda sun kulle hekwarae kungiyar dake Abuja.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:41 0:00

Facebook Forum

Bidiyo

Mijin Aljana A Kano: Shin Dama Aljanu Na Da ATM’ Na Kudi?
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:04 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG