Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yansandan Bangladesh Sun Kama Mutane Dubu Biyar


'Yansandan Bangladesh da suka yi ikirarin cafke mutane dubu biyar

Biyo bayan hare haren da masu tsatsauran ra'ayi da suke da alaka da ISIS suka dnga kaiwa sunakashe mutane tare da datse kawunansu, 'yansandan, a cikin samamen kwanaki uku da suka yi sun cafke wadanda suka kira bata gari

A kasar Bangladesh, Yansanda suka ce sun kama fiyeda mutane dubu biyar, wadanda ake zargi bata gari ne,a cikin kwanaki uku na samamen da suka kai a duk fadin kasar, a zaman martani na hare haren da tarzomar masu tsatsauran ra'ayin addinin musulunci suke kaiwa wasu tsiraru mabiya wasu addinan, da kuma 'yan ba ruwana da addini a kasar.
Baturen 'Yansandan kasar Shahidul Hoque, da yake magana jiya Lahadi, yace kamen ya hada da masu tsatsauran ra'ayi su 85, kuma dukkan wadanda aka kama caji daya ake yiwa kowa.

Ana zargin mayakan sakai dangane mutuwar fiyeda mutum 30 a Bangladesh tun a farkon shekarar da ta wuce. Mabiya ISIS sun dauki alhakin kashe fiyeda mutane 20 cikin wannan adadi. Domin ko a makon da ya wuce, mayakan sakai na ISIS sun dauki alhakin kashe wani ma'aikacin wurin ibadar 'yan Hindu, da wani tsohon shugaban darikar 'Yan Hindu, da wani kirista dan kasuwa. Dukkansu uku an datse su ne har lahira. Haka nan an soki matar wani jami'in tsaro wanda yake yaki da ta'addanci da wuka sannan aka harbeta aka kashe ta.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG