Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yansandan Najeriya Sun Kama Masu Sace Mutane Tsakanin Kaduna da Abuja


Ibrahim K Idris babban sifeton 'yansanda

Rundunar 'yansandan Najeriya ta samu nasarar kama wasu gungun masu satar mutane wajen su arba'in kan hanyar Kaduna zuwa Abuja

Masu garkuwa da mutane kimanin su arba'in ne aka kama kan hayar Kaduna zuwa Abuja.

Baicin mutanen , 'yansandan sun samu cafke bindigogi da kwamfutoci da kayan wuya na mata masu tsada. Sun sami guraye da layu. Haka ma aka sami kayan mutane da suka sace.

Kakakin 'yansandan Mashud Jimoh yace kwanan nan babban sifetonsu Alhaji Ibrahim Idris ya kaddamar da wani rundunar yaki da masu satar mutane da fashi da makami.

Ko makon jiya 'yansandan sun cafke muggan mutane fiye da talatin a kan hanyar ta Kaduna zuwa Abuja.

Amma Sabo Imam Gashuwa mai bin hanyar yace lamarin garkuwa da mutane ya dan ragu amma wani dan kasuwa dake Abuja Alhaji Alkali Muhammed yace 'yansandan wani lokaci suna yin kitso da kwarkwata. Ya bada misalin wani da suke aiki da aka sace sai da suka biya kusan miyan uku kafin a sakoshi.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:17 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG