Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yara Da Matasa Sun Samu Sabuwar Dama A Najeriya


Yara kanana a wata unguwa mai suna Isale-Eko a tsakiyar birnin Lagos.
Yara kanana a wata unguwa mai suna Isale-Eko a tsakiyar birnin Lagos.

Asusun UNICEF ya bullo da wani sabon shirin tallafawa yara domin kwato hakkinsu ta hanyar sanya su cikin shirin kansu na rediyo.

Yara marasa galihu a Najeriya, sun samu wata sabuwar dama ta ba-sabam ba domin cin moriyar hakkinsu na fadin albarkacin baki ta hanyar wani shirin rediyon matasa da asusun UNICEF ya kirkiro.

Shirin mai suna “Voices From The Streets” (watau murya daga kan tituna) wani shirin rediyo ne na musamman da zai maida hankali kan yara dake zube kan titunan kasar su na bara ko talla, ko zaman kashe wando. Wasu yara su 47 sun shiga cikin wannan shiri a Lagos. Kungiyar Child-to-Child shi ya zabo yaran, wadanda aka yi kokarin sauya musu halin rayuwa, aka kuma kai su ga likitoci na jiki da kwakwalwa su na lura da lafiyarsu.

A cikin shirye-shiryen rediyon da yaran suke gudanar, har da na batun ko wanene ya fi kula da yara a gida, Uba ko Uwa? Ina ne aka fi sake, a gida ko a kan titi? Ta yaya fadar gaskiya ta taimaki yaro ko ta cuce shi? Da kuma batun abubuwan da zasu yi da a ce sune suek shugabancin kasar.

A titunan birnin Kano, kamar sauran sdassan yankin Arewacin Najeriya, akwai yara almajirai rike da kwanonin roba su na bara na abinci ko kudi. Iyayen wadannan yara su na tura su domin karatun addini, amma da yake makarantu da malamansu ba su da sukunin ciyar da su, yaran sukan bazu su na bara.

Wannan shirin rediyo na Ku Saurare Mu yana ba yaran damar yin magana kan gwagwarmayarsu. Masu tallafa ma shirin sune Gidan Rediyo Najeriya Kaduna, da Hukumar Yaki da Fataucin Mutane ta Najeriya, NAPTIP, da kuam wani shirin tallafawa yara almajirai da ake kira “Child Almajiri Empowerment and Support Initiative.”

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG