Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yara Masu Fama Da Ciwon Rashin Abinci Mai Gina Jiki A Arewacin Najeriya Sun Samu Babban Tallafi


Mata masu jarirai su na layin karbar agajin abincin yara a garin Koleram a Jamhuriyar Nijar.

Hukumar agajin jinkai ta Tarayyar Turai ta bayar da kimanin Naira miliyan 637 ga ofishin UNICEF na Najeriya domin ciyar da yaran a jihohi 7 na arewacin Najeriya

Yara kimanin dubu 54 masu fama da ciwon rashin abinci mai gina jiki a wasu jihohi 7 da suka fuskanci kwamfar ruwa a yankin arewacin Najeriya, zasu ci moriyar agajin gaggawa da za a samar da tsabar kudi Euro miliyan 3 (kimanin Naira miliyan 637) wanda Hukumar Agajin Jinkai Ta Tarayyar Turai ta bayar ga ofishin Asusun UNICEF na Najeriya.

Za a yi amfani da wannan kudin domin tallafawa gwamnatoci wajen jinyar yara masu fama da ciwon rashin abinci mai gina jiki a jihohin Kebbi, Sokoto, Katsina, Zamfara, Jigawa, Yobe da Borno. Wadannan jihohin su na bakin iyaka da Jamhuriyar Nijar da kasar Chadi, wadanda a bara suka yi rokon agajin abinci a bayan mummunan karancinsa da aka yi a sanadin karancin ruwan sama a yankin Sahel.

An yi amfani da kudin wajen sayen katon dubu 53 da 730 na hadadden abinci mai gina jiki wanda ake amfani da shi wajen jinyar yaran dake fama da mummunan ciwon rashin abinci mai gina jiki. Tuni har yara kimanin dubu 40 sun ci moriyar wannan shirin.

Wannan shiri dai na hadin guiwa ne a tsakanin gwamnatocin jihohin da ta tarayya da kuma Asusun tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF. Da farko, shirin ya ta'allaka ne kan wasu al'ummomi 15 a jihohin Gombe da Kebbi da Sokoto, amma yanzu an fadada shi zuwa ga al'ummomi 145 a jihohi 7. An samu damar fadada wannan shirinb ne a saboda tallafin kudin da aka samu daga Hukumar Agajin Jinkai ta Tarayyar Turai, ECHO a takaice.

Asusun na UNICEF yace manyan abubuwa uku dake janyo ciwon rashin abinci mai gina jiki sune rashin abinci, da rashin dabi'a mai kyau ta kula da yara da kuma rashin wadatar ayyukan kiwon lafiya.

XS
SM
MD
LG