Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yara Milyan 9 Ne Ba Sa Makaranata A Yankin Arewa-Gwamna Kashim na Jahar Barno.


Gwamna Kashim Shettima Da Janar Tukur Buratai

Gwamnan ya bayyana haka ne lokacinda ya karbi bakuncin 'yar fafutukar ilmi Malala Yusufzai.

Gwamnan jahar Barno Kashim Shettima yace akwai yara milyan tara arewacin kasar wadanda basa zuwa makaranta a yankin, domin haka ya zama wajibi ga hukumomi a yankin su zuba jari ta fuskar Ilmi.

Gwamna kashim Shettima ya bayyana haka ne lokacinda ‘yar fafutukar ilmin diya mata, ‘yar kasar Pakistan wacce mayakan sakai na Taliban suka harba a kai, saboda dagewa kan ilmin diya mata.

Gwamnan yace idan ba don ilmin zamani ba da watakil yanzu yana can yana malamin makrantar allo, ko kuma yana can kauye yana kiwon dabbobi.

Gwamna Shettima, ya jaddada muhimancin ilmin diya mata.

Tunda farko a cikin nata jawabin, Malama Yusufzai, tace taje yankin ne da zummar duba yadda ita da wasu kungiyoyi masu rajin ilmin diya mata zasu aiki tare wajen kawo ci gaban ilmin diya mata.

Malama ta bayyana damuwa ganin Najeriya ce take da yara wadanda suka kai shekarun shiga makaranta amma basa basa zuwa neman ilmi.

Malama Malala tace ilmin shine turbar ci gaba, kuma taje yankin domin ganin ‘yan uwanta matasa ba’a barsu a bay aba, ta fuskar ilmi.

Wakilin Sashen Hausa Haruna Dauda Biu ne ya aiko manada wannan rahoto.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG