Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yar jejeniya da 'Yan siyasa Itace Mafita Kamin a Zabesu

Wasu matasa 'yan banga suka tsaya don a dauki hotonsu a Maiduguri, 11 Yuni, 2013.
Wasu matasa 'yan banga suka tsaya don a dauki hotonsu a Maiduguri, 11 Yuni, 2013.

Ganin yadda zabe ke kara gabatowa, wasu kungiyoyi masu zaman kansu sunci damara domin wayar da kan matasa dangane da rawar da yakamata su taka a wanna zaben mai zuwa. A cewar shugaban wata kungiya Mal. Murtala Adogi, yakamata matasa su mai da hankali kan chan-chanta ne ba jam’iya ba, saboda a lokutta da dama maganar jam’iya shike sa mutane cikin wani hali na ha’ula’I, yace dai mutane su duba suga wanene ke takara ba wai mecece jam’iyar da ta tsaidashi ba.

Ya yi nuni da cewar mafi akasarin jam’iyu sukan tsaida wasu ‘yantakarar da basu chan-chanta ba amma saboda wasu ra’ayin tsuraru a jam’iyar sai a bama wanda bai dace ba. Don haka mutane yakamata su sani wannnan karon ba maganar jam’iya bace maganar waya dace a zaba ce.

Ya kara da cewar yakamata a dinga yin yarjejeniya da 'yantakara, da cewar me zaiyi idan aka zabeshi wanda daga bisani idan bai cika alkawalin hakan ba sai a yi maganar kiranye. Yace su ba su da alaka da 'yan siyasa don haka suna kira ga matasa da su gujema yin siyasar kudi, don wannan ba zai kai su ko ina ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00
Shiga Kai Tsaye

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG