Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Na Aiki A Syria


A Bangladeshi survivor reacts after being rescued by firefighters from a burning office building in Dhaka.
A Bangladeshi survivor reacts after being rescued by firefighters from a burning office building in Dhaka.

Sa’o’i kadan bayan da aka fara aiwatarda yarjejeniyar tsagaita wuta a Syria, Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya ce ayyana wannan tsagaita wuta kila itace dama ta karshe ta maido da zaman lafiya a Syria bayan yakin basasa na shekaru biyar da kasar ta yi fama da shi.

Duk da cewar an fara samun kwanciyar hankali, akwai fadace fadace nan da can, Sakatare Kerry ya fada a jiya Litinin cewa , ba za a yi saurin tabbatar da ingancin yarjejeniyar tsagaita wutar da aka kulla tsakanin Amurka da Rash aba tukuna.

A ranar Asabar ne Sakatare Kerry da mininstan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov suka bayyana yarjejeniyar a Geneva, kuma yarjejeniyar ta samu goyon bayan wasu kasahe kamar Iran wacce take goyon bayan gwamnatin Syria da kuma Turkiya wacce ita kuma take son ganin an tsige shugaba Bashar al Assad daga mulki.

Idan aka yi mako daya da tsagaita wutar karkashin wannan yarjejeniya, hakan zai yi sanadiyar Amurka da Rasha su hada kai wurin kai farmaki ta sama a kan mayakan IS da al-Nusrat wacce ke kiran kanta da Jabhat Fateh al-Sham da aka dauketa reshen kungiyar al-Qaida.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG