Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Ake Hawan Arafat


Mahajjata a masallacin Namira da ke Arafat sanye da takunkumin rufe baki da fuska yayin aikin Hajjin bana, a daidai lokacin da duniya ke fuskantar annobar coronavirus
Mahajjata a masallacin Namira da ke Arafat sanye da takunkumin rufe baki da fuska yayin aikin Hajjin bana, a daidai lokacin da duniya ke fuskantar annobar coronavirus

A wani muhimmin mataki na aikin Hajji, alhazai sanye da takunkumin rufe baki da hanci domin kaucewa yada cutar Coronavirus sun isa Arafat, wani tsauni da ke kusa da Makka, birnin da ya kasance mafi tsarki ga mabiya addinin Islama.

Sun isa yankin ne domin sauke wannan farali da ya kasance mai matukar muhimmancin cikin ayyukan Hajji da ake yi a kasar Saudiyya a duk shekara.

Annobar cutar coronavirus ta sa yi tasiri kan aikin Hajjin na bana, wanda a shekarar da ta gabata ya samu halartar mutum miliyan 2.5 daga sassan duniya.

A wannan shekarar an takaita adadin mahajjatan tare da daukan tsauraran matakan dakile yaduwar cutar.

Bayan alhazan sun kwashe yinin ranar Alhamis suna addu'o'i, za kuma su nausa zuwa Muzdalifa, mai tazarar kilomita 5.5 daga filin na Arafat.

A ranar Laraba, wani rukunin Musulmai da ba su da yawa ya isa birnin Makkah domin fara gudanar da aikin hajjin bana.

An rage adadin wadanda za su iya halartar aikin Hajjin na bana sakamakon yadda annobar coronavirus ta mamaye duniya.

Maimakon sama da mutum miliyan 2 da ke zuwa aikin hajji a kowace shekara daga sassan duniya, hukumomin kasar sun takaita aikin hajjin banan ga ‘yan kasar Saudiyya da baki mazauna kasar mutum 1,000 kacal, wadanda aka tantance a makonnin da suka gabata.

An yi wa mahajjatan da shekarunsu suka kasance tsakanin 20 zuwa 50 gwajin cutar COVID-19 gabanin shigar su Makkah, inda aka bukaci su killace kansu tsawon mako 2 a dakunan otel dinsu, kafin su iya gudanar da aikin hajjin.

Yadda ake gudanar da aikin Hajjin
Yadda ake gudanar da aikin Hajjin

Musulmi a duk fadin duniya na zuwa aikin Hajjin ne domin cika daya daga cikin shika-shikan musulunci wanda akalla ake so mutum ya yi sau daya a rayuwarsa zuwa wannan wuri mafi tsarki ga mabiya addinin Islama.

Bayan wadanda suka je Hajjin a wannan shekarar sun kammala aikin nasu, an bukace su da su sake killace kansu na tsawon mako guda domin tabbatar cewa basu kamu da cutar ba a yayin Hajjin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG