Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Ce Ranar Karrama Majalisar Dinkin Duniya Wadda Aka Kafa a Shekarar 1945


Taron Majalisar Dinkin Duniya, MDD

Majalisar Dinkin Duniya, wacce aka kafa a shekarar 1945, yanzu tana da wakilai 193 kuma ana gudanar da ayyukanta ne bisa manufofin dake cikin daftarinta

A shekarar 1945 aka kafa Majalisar Dinkin Duniya wadda babban burinta shi ne hada kawunan kasashen duniya tare da kare ‘yancin kowa a duniya.

Nahiyar Afirka tana da wakilci na kasashe 52 kwatankwacin kashi 28 cikin dari na yawan wakilan majalisar. Wannan shi ya sa nahiyar Afirka ta wuce duk nahiyoyin duniya a yawan wakilai.

Ayyukan majalisar sun hada da tabbatar da zaman lafiya, aikata gaskiya da kuma dasa tubali na dindindin da zai samar da hadin kan duk duniya.

Commrade Abdullahi Koli, tsohon shugaban kungiyar kwadagon jihar Bauchi, ya bayyana wuraren da ya kamata majalisar ta maida hankalinta a nahiyar Afirka. Yace babban korafin kasashen Afirka akan shugabanci ne saboda irin al’adun nahiyar da tattalin arziki. Akwai kuma matsalar talauci da sau tari kan kawo tashin-tashina. Ya kuma yi kira ga majalisar ta taimaka wa matasa su samu aikin yi.

Shi kuwa Dr Shuaibu Muhammad Ado na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi, so yake majalisar ta tausaya wa kasashe masu karamin karfin tattalin arziki, ta hanyar yafe musu basusukan da ake binsu. Ya kamata kuma su kula da shugabannin Afirka dake sace kudi suna kaiwa kasashen turai.

Abdulwahab Muhammad nada karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG