Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Hukumomin Kiwon Lafiya Suka Kaddamar da Allurar Rigakafin Cutar Zangai A Nijar


Yaki da cutar zangai ko haukar karnuka da aka kaddamar a Yamai yau
Yaki da cutar zangai ko haukar karnuka da aka kaddamar a Yamai yau

Yau ce ranar cutar zangai da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe ta dalilin haka ne a Nijar hukumomin kiwon lafiya na mutane da dabbobi suka kaddamar da bada allurar rigakafin cutar kyauta ga dabbobi musamman karnuka.

Alkalumman hukumar kiwon lafiya ta duniya ko WHO sun nuna mutane kimanin dubu sittin ne ke mutuwa a duk fadin duniya kowacce shekara sanadiyar cutar akasarinsu kuwa yara ne.

Duk wadanda ba'a yiwa allurar rigakafi ba idan karnuka dake dauke da cutar, wadda kuma ake kira haukar karnuka, suka ciji mutane to zasu kamu da ita.

Biyo bayan samun yawan koke koke daga wadanda karnuka suka ciza ya sa hukumomin kiwon lafiyar dabbobi da na mutum suka fito suka kaddamar da bada rigakafin cutar ga mutane da karnuka kyauta yau.

Dr. Sani Gambo daraktan ma'akatar kiwon lafiyar dabbobi dake Yamai yace a likitance idan mutum ya kamu da ciwon zangai sai ya dinga yin miyau idan kuma kare ne sai yayi ta gudu. Karen ba zai ji tsoron komi ba ko kuma ya tsaya. Cikin kwana biyu ko ukku da farawa sai karen ya mutu. Yace matsala ce ta gaske. Da zara sun sami mutum da kare ya ciza sai wurin likitan mutane.

Yaki da cutar zangai ko haukar karnuka ta yiwa karnuka allurar rigakafi
Yaki da cutar zangai ko haukar karnuka ta yiwa karnuka allurar rigakafi

Idan kare ya ciji mutum kamata yayi a kama karen a kai wurin likita mai kula da dabbobi inda za'a rikeshi na kwanaki goma sha biyar. Idan bai mutu ba to sai su sakeshi, wato bashi da cutar.

Likitocin kiwon lafiyar mutane sun ce da zara kare ya ciji mutum to nan take a je karban magani. Wannan ita ce hanya daya tilo ta kaucewa mutuwa daga cutar zangai.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG