Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Laraba Ma'aikata Masu Yajin Aiki A Afirka Ta Kudu Zasu yanke Shawara


Ma'aikatan gwamnatin Afirka ta Kudu su na zanga-zanga lokacin yajin aiki

An shirya kungiyoyin ma’aikatan da kuma mashawartan gwamnati zasu kara tattaunawa a yau laraba.

A yau laraba ne ake sa ran watakila ma’aikatan gwamnati dake yajin aiki a Afirka ta Kudu zasu yanke shawara a kan ko zasu yarda da sabon tayin karin albashin da gwamnati ta yi musu domin su kawo karshen yajin aikin makonni biyu.

An shirya kungiyoyin ma’aikatan da kuma mashawartan gwamnati zasu kara tattaunawa a yau laraba.

Sabon tayin da gwamnatin ta yi musu na karin kashi 7 da rabi cikin 100 ne a albashinsu maimakon tayin karin kashi 7 daidai da ta yi musu a baya. Har ila yau, gwamnatin tana tayin karin alawus na gida da ta ke ba ma’aikatan daga dala 96 (kimanin Naira dubu 14 da dari 4) zuwa dala 109 (kimanin Naira dubu 16 da 360) a kowane wata.

Kungiyoyin ma’aikatan na gwamnati sun bukaci karin albashi na kashi takwas da digo 6 cikin 100 da kuma alawus na gida wanda ya zarce wanda aka musu tayi.

Wannan yajin aiki da ma’aikatan gwamnati su miliyan 1 da dubu 300 suke yi ya sa an rufe makarantu, yayin da likitoci na soja suka karbi ayyukan gudanar da asibitoci.

XS
SM
MD
LG