Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Za a Fara Sauraren Bayanan Shedu Game da Sharaar Da Ake yiwa Dan Wasan Kwaikwayon Nan Mai Suna O.J Simson


Kano Police arraigns 57 suspected rapists at Magistrate court 18 of Nomansland Court, in Kano, Nigeria November 17, 2015. Picture taken November 17, 2015.

Bayan ya kwashe kusan shekaru tara a gidan yari, tauraron wasanin da wasanin kwaikwaya irin na sinima O J Simpsom, yau Alhamis aka shirya, za a fara sauraren bayanan ko kuma shedun da kila zasu kai ga sakin shi a ranar daya ga watan Oktoba, idan Allah ya kaimu.

Simpson mai shekaru 70 a duniya, an yanke masa hukunci ne a kan laifin yin fashi da makami da sace mutum a shekarar 2008 biyon bayan tinkarar wasu dilalan kayayyakin wasanni guda biyu a shekarar 2007 a kan wasu kaya da shi Simpson yace an sace su daga wurinsa ne. An yanke masa hukunci shekaru tara mafi kankanci daga cikin hukuncin shekaru 33 a gidan yarin

Ya yi fice a fannin tallace tallace da kuma shirya fina-finai kamar wasan barkwanci na Naked Gun kana ya gudanar da shirye shiryen wasannin motsa jiki a telbiji da ake kira Monday Night Football, kafin aka kashe matarsa Nicole Brown Simpson da abokinta Ronald Goldman a shekarar 1994.
Da farko an zargi Simpson da aikata wannan kisar amma sai aka wanke shi daga wannan zargi a shekarar 1995.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG