Samar da daidaito tsakanin jinsunan maza da mata, shi ne zai zamanto batun da za a fi mayar da hankali akai yayin da a yau za a fara bikin ranar mata ta Duniya.
Taken wannan shekarar shi ne #EachforEqual – wato samar da daidaito a tsakanin kowa da kowa.
Samar da daidaito a tsakanin jinsuna da fagen siyasa da samun damar shiga kafafen yada labarai da fannin kiwon lafiya da kuma wuraren aiki, na daga cikin muradun da wannan ranar ta mata za ta fi mayar da hankali akansu.
Kiyasi dai ya nuna cewa, mata suke da kusan rabin adadin al’umar duniya, amma duk da haka, sukan gaza samun wakilcin da ya kamace su, musamman a fagen shugabanci, kamar yadda wani rahoton da cibiyar bincike ta Global Gender Gap ya nuna.
"Babu yadda za a samu ci gaba a fannonin tattalin arziki da harkokin yau da kullum, idan aka yi watsi da kashi 50 na al’umar duniya,” a cewar Ambasada Philip Carter, shugaban Mead Hill Group, wata kungiya da ke ba da shawarwari kan al’amuran yau da kullum.
Sai dai rahoton ya ce, lura da yadda ala’maura ke gudana, sai nan da sama da shekara 99 kafin a samu irin daidaiton da ake bukata.