Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Take Ranar Yaki Da Bauta A Duniya


Yadda ake bautar da kananan yara a Myanmar

Majalisar Dinkin duniya ta ware duk ranar biyu ga watan Disambar kowacce shekara a matsayin ranar yaki da bauta.

Jamhuriyar Nijar na daga cikin kasashen da da masana suka bayyana a matsayin kasar da ke fama da wannan matsala, wanda a baya bayan nan aka gano wani salon bautar zamani.

Dabi’ar bautar da dan Adam cikin salon gargajiya wata matsala da ta samu gindin zama shekaru masu yawa a jamhuriyar Nijar. Saboda wasu dalilan da ake dangantawa da al’adu ko na addini lamarin da yasa kungiyoyin fafutuka suka dage don tayar da hukumomi daga barci sai dai kuma har yanzu ana fuskantar turjiya.

Talauci da jahilcin da ake fama da shi a galibin yankunan kasar Nijar na daga cikin dalilan dake mafarin bunkasar sabon salon bautar da masana suka kira bautar zamani, a cewar Hajiya Halima Sarmai kusa a kungiyar yaki da masu gallazawa mata da yara kanana.

Gwamnatin Nijar ta kafa dokar haramta bauta tun a shekarar 2003, amma kuma matsalar ta zamanto tamkar ana hura mata wuta, dalili kenan da kungiyoyin kasa da kasa masu rajin kare hakkin dan Adam suka shawarci gwamnatin da ta sauya salo.

Domin karin bayani saurari rahotan Sule Mumuni Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:23 0:00

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG