Shaidu da kuma jami’ai a Mogadishu, babban Birnin Somaliya, sun ce wani harin bam na kunar bakin wake da aka boye cikin mota, ya kashe mutane akalla 10, ya raunata wasu 18.
Kungiyar ‘yan tsagera ta al-Shabab ta dauki alhakin wannan hari na yau talata da aka kai kan wani ginin gwamnati a gundumar Wadajir ta babban Birnin.
Wata karamar bas da aka shake ta da bam, ta kara da wannan gini da misalin karfe daya saura minti 20 na rana agogon kasar a yau Talata, a yayin da wasu matasa da mata ‘yan raji suke yin taro a ciki.
Shaidu suka ce direban ya banke kofar shiga ginin, sannan ya tayar da wannan bam mai karfin gaske.
Daga cikin wadanda suka ji rauni har da kwamishinan gunduma Omar Abdullahi Hassan, da shugabar kungiyar mata da shugaban kungiyar matasan da kuma sakataren gunduma.
Masu aikin ceto suna amfani da motocin buldoza a kokarin samo wadanda suke da rai da kuma gawarwaki.
Facebook Forum