Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Tsohon Zakaran Wasan Kwallon Kafa Ya Zama Sabon Shugaban Liberiya


Sabon shugaban Liberia George Weah a farar riga yayinda ake rantsar dashi tare da tsohuwar shugabar kasa da ta mika masa mulki Ellen Johnson Sirleaf

Yau Liberiya ta yi sabon shugaban kasa yayinda aka rantsar da tsohon zakaran wasan kwallon kafa George Weah wanda ya maye gurbin tsohuwar shugabar kasa Ellen Johson Sirleaf

Tsohon zakaran wasan kwallon kafa, George Weah, dan shekara 51 da haihuwa, ya zama sabon shugaban Liberiya bayan da aka rantsar da shi yau Litinin a wani biki da aka yi a katafaren filin wasan dake babban birnin kasar Monrovia wanda ya cika makil da jama'a.

Shugabannin kasashen Gabon, Ghana da Saliyo suka kasance wurin rantsar da George Weah.

A cikin jawabinsa sabon shugaban ya ce "Na kwashe shekaru da dama a rayuwa ta ina wasa a filayen kwallo, amma yau ina ji wani iri ne daban da babu irinsa", in ji shi. Ya yiwa shugabar kasar mai barin gado Ellen Johnson Sirleaf godiya wadda ya ce "ta gina tushen da zasu iya tsayawa kai cikin lumana".

Sabon shugaban ya yi takara ne da tsohon mataimakin shugaban kasa Joseph Boakai wanda shi ma ya sauka bayan ya yi wa'adi biyun da kundin tsarin mulkin kasar ya kayyade.

Weah ya ce abun da zai fara tinkara shi ne yaki ba sani ba sabo da cin hanci da rashawa.

Bikin na yau Litinin shi ne na farko da za'a mika mulki cikin lumana a shekaru fiye da saba'in a tarihin kasar.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG