Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Wata Kotu A Michigan Zata Yanke Hukuncin Ko Pasto Jones Zai Yi Zanga A Harabar Masallaci


Babban Attoni Janar na Amurka Eric Holder

Yau jumma’a ce ake sa ran gungun masu taya alkali yanke hukunci a jihar Michigan dake arewacin Amurka zasu yanke hukunci ko pasto Terry Jones zai iya ci gaba da zanga zanga da ya shirya yi a yinin yau a harabar wani masallaci.

Yau jumma’a ce ake sa ran gungun masu taya alkali yanke hukunci a jihar Michigan dake arewacin Amurka zasu yanke hukunci ko pasto Terry Jones, zai iya ci gaba da zanga zanga da ya shirya yi a yinin yau a harabar wani masallaci mafi girma a Amurka dake birnin Dearborn.

Paston ya amince da zaman shari’ar,bayanda alkali ya bashi zabin ya bada jingina kamin ya gudanar da zanga zangar ko kuma a yi shari’ar bashi izini.

Da ya bayyana jiya Alhamis gaban kotu,Jones ya bayyanawa alkali damuwarsa na yin shari’ar ranar jumma’a da safe domin hakan yana iya hanashi damar yin zanga zangar idan shari’ar ta dauki lokaci.

Da misalin karfe 5PM na yamma agogon yankin,watau karfe 10 na dare agogon Najeriya,nijar da kamaru karfe 9 na dare agogon Ghana Jones yake shirin yin zanga zangar.

Pasto Jones ne limamin wata karamar majami’ar masu tsatstsaucin ra’ayi a Florida. Cikin watan jiya ne Pasto Jones ya kona al-Qur’ani,wadda ya janyo mummunar tarzoma a Afghnaistan.

XS
SM
MD
LG