Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Sake Jefa Kuri'a A Majalisar Amurka Don Neman Sauya Tsarin Inshorar Lafiya Ta Obamacare


Shugaban 'Yan Majalisar Amurka Masu Rinjaye Kevin McCarthy

Ranar Alhamis ake sa ran ‘yan majalissar wakilan Amurka za su jefa kuri’a akan batun soke tsarin inshorar lafiya wanda ake kira Obamacare tare da yin wani sabo.

Shugaban ‘yan majalissa masu rinjaye Kevin McCarthy ya bayyana kwarin gwiwarsa akan cewa suna da goyon bayan ‘yan jam’iyyar Republican da zai taimaka masu daukar wannan matakin, bayan da yunkurin hakan bai cimma nasara ba a cikin watan Maris din da ya gabata.

Shugabannin ‘yan jam’iyyar Republican, ciki har da shugaba Donald Trump, sun kwashe kwanaki suna kokarin neman goyon bayan ‘yan majalissa akan su jefawa sabon tsarin lafiyar kuri’a don a soke na Obamacare.

Wasu jigajigan jam’iyyar ta Republican su biyu, Fred Upton da Billy Long, sun fada jiya Laraba cewa zasu bada goyon baya ga sabon tsarin bayan da suka tattauna batun yin garambawul ga tsarin da fadar White House.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG