Yau uku ga watan Disamba wanda ya yi dai dai da ranar Nakasassu a Duniya. Majalisar Dinkin Duniya ta aminta da a ware wannan ranar a matsayin ranar Nakasassu ta Duniya a shekarar Alif dubu daya da tamanin da uku (1983). A wani kididdiga na Majalisar Dinkin Duniya kimanin kashi 10 cikin 100 ke fama da matsalar nakasa a Duniya, wanda yawan mutanen duniya suka kai kimanin Miliyan Dari Shida da hamsin, wanda adadin kimanin kashi 20 cikin dari ke fama da talauci.
Kimanin kuma kash biyar zuwa sha biyar ne kawai ke samun na’urori wadda ke tai makamusu don more rayuwarsu.
A cewar Mal. Sani Yusuf Fagge, yayi mana Karin haske dangane da matsalolin da mambobin su ke fuskanta. Yayi nuni da cewar wasu mambobinsu na da sana’o’ie da suke iyayi amma saboda rashin tallafi suna fuskantar damuwa, kuma gwamnati bata basu wata kulawa ta musamma ba.
Sun kuma yi ta rubuce rubuce amma dai har yanzu babu wani abu daga bangaren gwamnati. Ta bakin Alh. Usman Yusuf mai baiwa gwamna shawara a harkar nakasassu, yace gwamnati na iya bakin kokarinta taga cewar ta tai makawa duk masu bukata ta musamman.