Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yunkurin Jihar Kaduna Na Ciwo Bashi Ya Haddasa Yamutsi


Wasu matan Kaduna sun yi zanga zanga kan hana jiharsu cin bashi
Wasu matan Kaduna sun yi zanga zanga kan hana jiharsu cin bashi

Jihar Kaduna na cikin jihohin da suke neman ciwo bashi amma wannan lamarin ya rarraba kawunan ‘yan jihar inda har mata suka fito suna zanga zanga tare da dorawa Senator Shehu Sani laifin kawo cikas ga yunkurin

Yunkurin gwamnatin jihar Kaduna na ciwo bashi domin gudanar da wasu ayyuka na ci gaba da rarraba kawunan ‘yan jam’iyyar APC mai mulkin jihar.

Wasu mata da suka dorawa Senator Shehu Sani alhakin jawo jinkirin ciyo bashin sun fito sun yi zanga zanga a garin Kaduna, babban birnin jihar.

Daya daga cikin matan da suka yi zanga zangar, Hajiya Saratu Abdulaziz, ta yiwa manema labaru karin bayani, inda tace Senator Shehu Sani ya yi masu alkawarindaukaka daraja martabar mata kuma shi ne shugaban kwamitin dake da hakin amincewa da cin bashin amma ya ki sawa jiharsa hannu saboda wani dalilin dake zuciyarsa.

Amma Commrade Suleiman Ahmed dake taimakawa Senator Shehu Sani a kan harkokin siyasa, yana ganin wadanda ke zanga zangar basu binciki gano ko jihar Kaduna ce kadai ba’a ba bashin ba. Yaceakwai jihohi akalla goma da ba’a basu bashin baba. Ya kuma zargi masu zanga zangar da tallata wani mutum daban da suke cewa shi ya cancanta ya zama Senator din yankin. Ya ce har kudi aka dinga rabawa a wurin zanga zangar tare da yawo da kwalaye dake dauke da sunan wannan mutumen.

Yunkurin ciwo bashin ya sa wadanda suka raba gari da gwamnan Nasiru El-Rufai na jihar a jam’iyyar APC reshen jihar Kaduna su soki lamirinsa. A cewarsu babu wani dalilin ciwo bashin. Sunyi nuni de cewa a cikin shekaru 50 gwamnoni 19 da suka yi mulki a jihar sun ciwo bashin Naira biliyan 80 ne kawai, yayinda gwamnatin yanzu ke neman ci wa jihar kaduna bashin da ya kai dalar Amurka 350m, kwatankwacin Naira biliyan 122.

Sai dai Malam Muhammad Namadi dan majalisar wakilai daga jihar yana goyon bayan a ciwo bashin saboda za’a yiwa al’ummar Kaduna aiki da shi.

Ga rahoton Isah Lawal Ikara da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:37 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG